Za’a Ɗaure Matashiya kan Shigar Banza a Ƙasar Ruwanda
An gurfanar da wata mata ƴar kasar Rwanda mai shekaru 24, Liliane Mugabekazi, wadda aka kama a ranar 7 ga watan Agusta, bayan ta halarci wani shagalin biki sanye da rigar shara-shara a gaban ƙuliya.
Hoton Liliane wacce ta kasance a wurin kade-kade da shahararren mawakin Faransa, Tayc ya yi a kwanakin baya ya yi yawo a kafar sadarwa ta zamani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar ruwa ta ruguza Al’ummomi 225 a Kano da Jigawa — NEMA
Busingye Johnston wanda a halin yanzu shi ne jakadan Rwanda a Burtaniya a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi Allah-wadai da salon sanya tufafin Liliane, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da bai dace ba.
Ya rubuta cewa, “Batun samarinmu maza da mata da suke sha da muggan kwayoyi a sume, suna bayyana tsirara a bainar jama’a abin kyama ne.”
Mai magana da yawun masu shigar da kara, Faustin Nkusi ya ce matar ta aikata manyan laifuka saboda bayyana tsirara a bainar jama’a, yana mai cewa “tufa ce ta kunya”.
A cewar jaridar Rwanda, The Chronicles, an gurfanar da matar mai shekaru 24 a kotu ranar Alhamis.
Rahotanni sun nuna cewa lauyan Liliane ya bukaci kotun da a saurari karar a cikin kyamara.
Idan dai za’a tuna cewa a cikin Maris 2022, ‘yan sanda sun kama wata mata ‘yar shekara 20 saboda “buguwar jama’a da cin zarafi” bayan wani hoton bidiyo na kwance a kasa cikin shaye-shayen giya da aka yada a shafukan sada zumunta