Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa, kan mutuwar akalla bakin haure 23, wadanda suka mutu a ranar Juma’a yayin da dimbin jama’ar suka yi kokarin tsallakawa zuwa yankin Melilla na arewacin kasar ta Sifaniya.
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya ce, ya kadu tare da nuna damuwa game da yadda ‘yan ci-ranin Afirka ke yi a lokacin da suke yunkurin ketare iyakokin kasa da kasa.
Mista Moussa Faki Mahamat a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, ya tunatar da dukkan kasashen duniya wajibcin da ya rataya a wuyansu a karkashin dokokin kasa da kasa na mutunta dukkan bakin haure da kuma ba da fifiko ga tsaron lafiyarsu da hakkin dan Adam, tare da kauracewa amfani da karfin tuwo.
Hukumomi a Maroko sun ce wasu daga cikin wadanda suka mutu sun fado ne daga saman katangar kan iyaka da ta raba Morocco da yankin Melilla na kasar Sifaniya.
Rahotanni sun nuna cewa, sama da mutane 130 ne suka yi nasarar tsallake shingen.
Yankin Melilla Da Ceuta dake kasar Sifaniya na da iyaka da arewacin nahiyar Afrika, wanda shi ne ya hana dahiyar turai da kuma Afrika.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Bincike ya nuna cewa, yunkurin tsallakawar jama’ar a ranar Juma’a shi ne na farko tun bayan da Sifaniya da Maroko suka daidaita takaddamar diflomasiyya da ta shafe shekara guda ana yi a watan Maris.
Hakan na zuwa ne bayan Sifaniya ta goyi bayan shirin cin gashin kai na kasar Maroko ga yankin yammacin Sahara da ake takaddama a kansa.
A wani labarin kuma na daban.
Mista Muhammad Tanko yayi murabus cikin gaggawa, a cewar majiyoyin kotun koli guda hudu da suka zanta da Jaridar Peoples Gazette a safiyar ranar Litinin.
Mai magana da yawun kotun kolin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a safiyar ranar Litinin, amma ya ce za a yi karin bayani kan dalilinsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito a makon da ya gabata daga zanga-zangar da alkalan kotun koli suka rubuta kan Mista Tanko, inda ake zarginsa da cin hanci da rashawa da rashin da’a da kuma rashin kula da jin dadin ma’aikata.
Zarge-zargen da ba a saba gani ba, masu sharhi na kotun suna kallon su a matsayin abin fashewa a tarihi, suna masu gargadin cewa hakan na iya dagula mata suna.
Mista Tanko ya amsa wa alkalan kotun, inda ya zarge su da rawa tsirara a kasuwa tare da wanke kansa daga aikata wani laifi.