Za’a dakatar da Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi kan karɓar Bashi a Jihar Neja
Kwamitin majalisar dokokin jihar Neja da ta kafa domin duba lamunin bayar da bashin kudaden kwangila ga kananan hukumomi ashirin da biyar ya ba da shawarar dakatar da shugabannin ƙananan Hukumomi goma sha biyar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Yi Garkuwa Da Shugaban Karamar Hukuma A Gidansa
Majalisar ta dauki wannan mataki ne domin share fagen samun dama ga kwamitin ya gudanar da ayyukan shi yadda ya kamata.
Shugaban kwamitin, Abdulmalik Madaki Bosso a lokacin da yake gabatar da rahoton, ya ce Shuwagabannin ƙananan Hukumomi goma sha biyar sun hada da, Mokwa Gbako Suleja Gurara Tafa Paikoro Bosso Agwara Borgu Kontagora Wushishi Magama Mariga Mashegu da Rijau.
Ya ce matakin ya yi daidai da tanadin sashe na 128 da na 129 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima da kuma tanadin sashe na 90 karamin sashe na 1a da b da c na dokar kananan hukumomi ta 2001 da aka yi wa kwaskwarima.
Shugaban kwamatin ya yi zargin cewa galibin shugabannin ƙananan Hukumomi daya bada shawarar a dakatar sun karbi bashin ne ba tare da bin ka’ida ba wanda ya ce majalisar ba za ta amince da shi ba.
“Matsalar ta kara wani nauyi a kan gudanar da ayyukan kananan hukumomi a jihar,” in ji shi.
Sai dai Bosso ya kara ba da umarnin cire N8m kowacce daga kananan hukumomi domin biyan bashi da aka dakatar saboda gazawar ma’aikatar wajen samun kudurin majalisar kamar yadda sashe na 97 karamin sashe na 1 na dokar kananan hukumomi ta 2001 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.
A wani labarin kuma: Dalilin Da Ya Sa Dole Jam’iyyar PDP Ta Mutunta Mu – Gwamnan Rivers
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana dalilin da ya sa dole jam’iyyar PDP ta mutunta shi da sauran gwamnonin da ke tsaginsa sa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wike ya yi ikirarin cewa gwamnonin su ne ke yiwa jam’iyyar yakin neman zabe tare da ayyukan da suka aiwatar a jihohinsu daban-daban don haka sun cancanci a girmama su.