Gwamnatin Tarayya za ta fara ɗebo ‘yan Najeriya a yau Laraba da suka tsallaka zuwa ƙasashe maƙota daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta kasa ta fitar ta ce, ana sa ran rukuni na farko na mutanen za su dawo gida ne a gobe Alhamis.
Sanarwar ta ƙara da cewa zuwa yanzu hukumomi na da adadin ‘yan Najeriya da suka samu shiga Romania, Hungary, Poland da kuma Slovakia.
Ma’aikatar ta ce a kasar Hungary za’a kwaso akalla mutane 650, Poland – 350 Romania – 940, Slovakia – 150.
A wani labarin Kuma na daban.
Majalisar Dattijai ta zartar da ƙuduroriin gina Jami’o’i a Abuja, da Rivers
Majalisar Dattijai ta Najeriya ta zartar da wasu kuɗirai guda biyu domin gina Jami’o’i a Babban Birnin Tarayya, Abuja da Jahar Rivers.
Sune Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abuja,Abaji, da Jami’ar Tarayya ta Mahalli Koroma/Saakperwa Tai Ogoni, Jahar Rivers.
An dai zartar da ƙudirorin bayan yin dubi akan rahotanni guda biyu da Kwamitin Manyan Makarantu da TETFUND ya gabatar.
Mataimakin shugaban Kwamitin Sanata Sandy Onuh dayake gabatar da rahoton a madadin Shugaban Kwamitin, Ahmad Babba Kaita, yace ƙudirin gina Jami’ar Tarayya ta Kimiyya da Fasaha, Abaji, zai cike giɓin da ake dashi na ilmi a bangaren Kimiyya da Fasaha.
A cewar Sanatan, Ƙudirin gina Jami’ar Mahalli zai bayar da Fasaha ga Malamai da masu Son ƙwarewa, Wanda hakan zai sanya a riƙa bada shaidar karatun Digiri, dana biyu dana uku da sauran wasu karatuttuka , da bincike.
Dukkanin ƙudirorin an ƙaddamar dasu, bayan yin dubi akan kwamitin