Kungiyar samar da ruwan leda na sha wato ”Pure Water” ta ce yanzu haka ta shirya tsaf domin kara farashin ruwan.
Shugabar kungiyar ta kasa Miss Clementina Active ce ta sanar da hakan a wata Sanarwa da suka fitar a Abuja.
KU KARANTA: Ku zabi Tinubu don cigaba da ayyukan Buhari – Badaru
Ativie ta ce yanzu haka zasu kara kudin ruwan kowace leda daga Naira 200 zuwa Naira 300, ga duk jakar ruwan.
Ta ce daukar wannan mataki ya samo asali ne, bayan taron koli da suka da gudanar da ya’yan kungiyar Jiya Laraba a Abuja, kuma anan suka cimma wannan matsaya.
Karuwar farashin kayan da suke amfani da su wajen samar da ruwan ledar, na daga cikin abubuwan da suka tilasta musu ganin sun kara farashin.
A wani labarin kuma: Peter Obi Bai Kai Darajar Kobo 10 Ba – Gwamna Sule
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi watsi da kididdigar yanar gizo da ta sanya Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour a gaban Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da kuma dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Sule ya yi ikirarin cewa sukar Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, da gwamna mai ci, Charles Soludo ya yi, wanda ya rage darajar Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa da kasa da kobo 10.