An sanar da karo Jami’an tsaro na Yan sanda dubu biyu da dari biyar don samar da tsaron kan zaben da za’a gudanar a Legas a ranar Asabar. Jaridar Channel Tv ta wallafa a shafinta
Shugaban hukumar zabe ta Jahar Legas, Justice Ayo Philips, ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channel Tv.
Philip yace shugaban jami’an tsaro na Jahar Legas ya bata tabbacin haka.
karanta:- An tasa keyar Sunday Igboho zuwa kurkukun Jamhuriyar Benin har sai makon gobe
“Muna aiki tukuru da sauran Jami’an tsaro tun daga kan Yan sanda,. Jami’an sojojin sama, dana ruwa, dana kasa, da Jami’an tsaro na farin kaya da sauran Jami’an kasar nan don bukasa tsaro a Jahar.”
“Mun san yanayi na halin rashin tsaro dake addabar yankin, a jiya munyi waya da shugaban Yan sanda na Jahar zai samar da karin jami’an tsaro dubu biyu da dari biyar don inganta tsaro wajan gudanar da zaben.” Kamar yadda ta bayyana.
Ta cigaba da cewa “Muna fatan za’a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, masu zabe su kada kuri’arsu sannan su tafi izuwa wajan kasuwancinsu.”
Sai dai a yayin da ake kokarin gudanar da zaben, jimillan jam’iyyu guda goma sun kai Karar hukumar zaben ta Jahar Legas don dakatar da zaben.
Sai dai babban kotun dake Jahar Legas tayi watsi da kudirin nasu.
Shugaban Alkalai na Jahar Legas, kuma babban mai Shari’a a Najeriya, Moyosore Onigbanjo, shima ya misanta kudirin nasu.
Moyosore Onigbanjo, yace basu da wani gamsassun dalilai da za su gamsar da Kotun.
Ita dai babban kotun ta dawo da shari’ar izuwa wata Karamar kotun dake Jahar Legas.
Sai dai itama Karamar Kotun ta yanku hukuncin irin wadda babban kotun ta yanke.