Za’a koyawa Mata Yan gudun hijira sama da dubu biyu dinki da hada sabulu a Zamfara
Wata Kungiya mai zaman kanta ta dauki nauyin koyawa mata dinki da hada sabulu da sauran sana’oi daban-daban a fadin jahar.
Ana sa ran cewa aikin zai tallafa wa mata da yara kimanin dubu biyu dake zaune a wajan gudun hijira da samun basira domin ruke kawunansu.
Karanta:Rundunar Hadin Gwuiwa, ta kashe yan ta’addan ISWAP da dama a Borno
Fatima Shinkafi Sakatariya ta ma’adanan kasa Kuma jagora ga Umaru Shinkafi Foundation ta bayyana hakan lokacin da ta kai ziyara a wajan Yan gudun hijira dake Tsunami a Gusau Jahar Zamfara.
Akwai Mata da yara sama da dubu biyu dake zaune a gidan Yan gudun hijira Wanda sun rasa muhallin su sanadiyyar Yan ta’adda da Bokoharam suke farmakar yankin.
Da akwai Yan gudun hijira da suke a gidan sama da wata uku wanda sun rasa jindadinsu.
Fatima Shinkafi Jagoran Umaru Shinkafi Foundation tace wannan kungiyar zata tallafawa Mata wanda koda sun koma gidajen su zasu sami sana’oi da zasu rinkayi.
Ta kuma jawo hankalin su dasu cigaba dayin sana’oi da aka koyawa musu Koda sun koma gidajen su domin rike kansu.
Bashir Ahmad kuma cewa yayi wannan taimakon anyi shine don rage musu radadi da kuma sanya murmushi a fuskan su.
Yan gudun hijira sun nuna godiyarsu da jindadin kan irin wannan tallafin, sun kuma sha alwashin cigaba da yin ayyukan da za’a koyar dasu.
Comments 1