Juventus ta bayyana cewa Federico Chiesa yana jinyar raunin da ya samu a gabansa bayan da ya ji rauni a gwiwa a wasan da kungiyar ta doke Roma a ranar Lahadi.
Dan wasan na Italiya mai shekaru 24 ya fito ne a farkon rabin wasan bayan ya karo da Ainsley Maitland-Niles na Roma.
An taimaka masa wajen fitar da shi daga filin wasa tare da maye gurbin sa da Dejan Kulusevski.
Da take bayar da karin haske, Juventus ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa, za a yi wa dan wasan tiyata nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
“A yayin wasan na jiya, Federico Chiesa ya ji rauni sosai a gwiwarsa ta hagu.
“Gwajin binciken da aka yi a safiyar yau a ya nuna raunin da ya samu na gaba ne.
“Ya zama dole a yi wa dan wasan tiyata nan da ‘yan kwanaki masu zuwa,” in ji kulob din.
Comments 1