Shugaban tsarin yiwa kasa hidima ta NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya shawarci masu yiwa kasa hidima a jihar Bayelsa da su tsere idan suka ga ta rincabe a lokacin gudanar da zaben da za a yi a jihar Bayelsa a ranar 16 ga watan Nuwamba. Ya bayyana haka ne a wata takardar manema labarai da ta fito ta hannun Kakakin NYSC, Adenike Adeyemi a ranar Jumma’a.
Ya kara da basu shawara da su nemi hanyar ficewa a duk wani waje da za su yi aiki.
“Ku gudu don ceton rayuwarku idan kuka ga abubuwa sun rincabe sannan ku guji shiga wurare masu hadari. Ku kasance masu ladabi da nutsuwa ko an bata muku rai a lokacin mu’amala da masu kada kuri’a kuma ku tabbata wayoyinku a cikakken caji da isasshen kudin kira a lokacin zaben.
“Kuma ku tsaya a matsayinku na ‘yan-babu-ruwanmu. Saboda ba zamu lamuncewa duk wanda ya sabawa dokar zabe ba,”inji shi.
Kafin nan a takadar manema labaran da Kakakin NYSC din, Adenike Adeyemi ta fitar an ruwaito ce Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yana tabbatar wa da masu yiwa kasar hidima cewa sun tanadar da jami’an tsaron da za su basu kariya a gidajen da suke kwana.
Ya kuma ce sa masu yiwa kasa hidima a harkar ta zabe yana kara wa mutane aminci da hukumar, kuma yana nuni da zaben babu cuta babu cutarwa.