An tsaurara tsaro a hedikwatar INEC da ke birnin Lokoja na Kogi.
Jami’an tsaron na dauke da makamai da kayan aiki domin su tabbatar da tsaro sosai a ofishin hukumar zaben.
Tuni dai INEC ta fara rarraba kayan zaben zuwa kananan hukumomi 21 na jihar, don tabbatr da cewa an fara zaben a kan lokaci a gobe.
Kusan mutum miliyan 1.4 ne ake sa ran za su kada kuri’unsu.