Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan IGP Usman Alkali ya ce sama da jami’an tsaro 400,000 ne za a tura domin gudanar da zabukan da ke tafe domin tabbatar da gudanar da atisayen cikin sauki a fadain kasar nan.
Alkali ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya bayyana a taron manema labarai na ministoci da tawagar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa, a Abuja.
IGP ya ce daga cikin wannan, ‘yan sanda za su samar da sama da jami’ai 300,000 yayin da za a samu cikamakin daga sauran hukumomin tsaro a kasar.
Shugaban na ‘yan sandan ya zayyana wasu barazana ga yadda zaben ke gudana da suka hada da karancin man fetur da kuma kudade amma ya ba da tabbacin cewa za a daidaita lamarin kafin a fara atisayen.
“Muna da tabbacin yanayin kudi da man fetur za su daidaita kafin gudanar da zaben,” in ji shi.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Alkali ya tabbatar da cewa, akwai wata runduna ta leken asiri da za ta bi diddigi tare da kamo wadanda ka iya shiga harkar siyan kuri’u da sauran masu son kawo cikas ga aikin.
A Wani Labarin Kuma APC Ta Buƙaci A Yi Gaggawar Canza Wani Kwamishina
Jam’iyyar APC reshen jihar Osun, ta bukaci da a gaggauta can zawa kwamishinan ‘yan sanda, Patrick Kehinde Longe wurin aiki.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Laraba a Osogbo.