Yanzu haka dai kusan kwanaki takwas ya rage a gudanar da zaben 2023, jam’iyyar NNPP, dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Kwankwaso ya bayyana irin ‘yan takarar da bai kamata ‘yan Najeriya su goya musu baya ba.
Kwankwaso ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su goyi bayan ‘yan takarar da ake da shakku kan takardar shaidar karatunsu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin Tsaro Ba Zai Shafi Jadawalin Zabe A Jihar Zamfara Ba – INEC
Da yake jawabi a wani taro da dalibai a garin Keffi na jihar Nasarawa, Kwankwaso ya kuma yi gargadin a guji marawa ‘yan takara da sabani kan shekarun su.
Kwankwaso ya ba da shawara, “Kada ku tallafa wa mutanen da ba su da takardun shedar karatu kuma waɗanda ba su san shekarun su ba.
“Kada ku goyi bayan mutanen da idan ka tambaye su game da shekarunsu, suna jin zafi, kuma kada ka goyi bayan mutanen da suke son tilasta wa mutane irin su.
“Abin takaici ne matuka a ce muna da kasa mai rabe-rabe. Zan mai da WASSCE da NECO kyauta ga duk ’yan Najeriya, kamar a baya, za mu tabbatar da tallafin karatu ga dalibai inda yaran talakawa za su iya zuwa makaranta.”
A wani labarin kuma, Buhari Yana Kokarin Kawo Cikas Ga Dimokuradiyyar Najeriya Wajen Sake Fasalin Naira – Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da burin murguda dimokuradiyyar Najeriya tare da sake fasalin tsarin Naira na babban bankin Najeriya.
Ganduje ya yi wannan zargin ne a wani taro na kungiyar Tsoffin ‘yan Majalisu ta shiyyar Arewa maso Yamma a Kano cikin makon.