Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma sanata mai wakiltar Jihar Kano ta tsakiya a zauren majalisar Dattijai Rabiu Musa Kwankwaso, yace kudade aka rabawa Yan Majalisun dokokin Jihar Kano suka bayar da goyon baya aka rarrraba Masarautun Jihar Kano.
A wata tattaunawa a gidan sa dake Kano a daren Jiya Laraba da manema Labaru, Kwankwaso ya bayyana rarraba masarautun Kano a matsayin rashin sanin darajar manyan gari ne ya sa gwamnatin jihar Kano ta yanzu ta kirkiro wasu sababbin masarauta a Kano.
Ayayin tattaunawar Dan-Musa, yace wannan matakin da gwamnatin Ganduje ta dauka ya lalata jihar Kano, kuma zai yi wa kowa illa nan gaba domin ana bukatar manyan Sarakuna masu daraja a kasa.
Yace fadin duniya gabaki daya kowa ya san Abba K Yusuf ne ya bayar da Ganduje a zaben Gwamnan Jihar Kano, duniya ta sheda haka.
Kan irin zaben da aka gudanar maganar gaskiya an zubar da Mutuncin Jihar Kano a idon duniya.