Wani dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa, ya bayyana hanya daya tilo da jam’iyyar adawar za ta yi domin samun nasara a zaben shekarar 2023.
Ohuabunwa, yayin da yake jawabi ga jiga-jigan jam’iyyar PDP a Minna a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, domin jam’iyyar ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2023, akwai bukatar ta ci gaba da yin kyakkyawan tsari wajen zabar shugabanninta.
“Don PDP ta lashe zaben shugaban kasa a 2023, dole ne ta yi abin da ya dace a daidai lokacin da ya dace wajen zaben shugabannin jam’iyyar,” in ji Ohuabunwa.
a kuma bayyana cewa karuwar talauci a tsakanin ‘yan Najeriya ne ya jawo wa Najeriya matsalar rashin tsaro da kalubalen zamantakewa da tattalin arziki.
Mai neman shugabancin kasar ya bayyana cewa hanyar da za a bi wajen magance wannan matsala ita ce ‘yan Najeriya su zabi shugaba mai wayewa, mai hangen nesa, kuma kwararre.
“Najeriya na bukatar shugaba mai kyawawan halaye da zai jagoranci kasar nan akan turbar adalci.
“Samar da yanayi mai ba da damar saka hannun jari zai kai ga samar da damammaki na kasuwanci, ayyuka, shirye-shirye da wadata al’umar kasar nan, domin kawar da talauci,” in ji shi.