Kungiyar matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun, ta zargi ministan harkokin cikin gida, Mista Rauf Aregbesola, da yin adawa da burin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a jihar.
Shugaban matasan jam’iyyar APC, Goke Akinwemimo, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a Osogbo, babban birnin jihar a ranar Larabar da ta gabata, ya sanar da shugaban jam’iyyar na kasa cewa Ministan ba ya cikin jam’iyyar APC.
Akinwemimo, ya bayyana fatansa na cewa Ministan da magoya bayansa ba za su yi nasara ba a shirinsu na kawo wa jam’iyyar cikas a zabukan da ke tafe.
Ya ce, “Muna fadin haka ne domin sanar da shugabannin jam’iyyarmu ta kasa cewa Aregbesola da abokansa ba sa tare da APC.
Tsaron Kasar Nan, Ya Fi Zaɓen 2023 Mahimmanci– Olawepo Hashim Ya Fadawa Buhari
“Baya ga cewa abubuwan da suka yi a baya sun nuna cewa suna yi wa ‘yan adawa aiki ne, haka nan kuma sun kuduri aniyar ganin mun fadi wasu zabukan da suka hada da na shugaban kasa.
“Suna shirin bayyana halaka ga jam’iyyarmu. Amma a shirye muke mu bijirewa su kuma ba za su yi nasara ba”.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, Aregbesola, wanda a baya-bayan nan ya yi taho-mu-gama da tsohon gwamnan jihar Legas, shi ma an saka masa yatsa a kan gazawar jam’iyyar ta lashe zaben gwamnan da aka yi a watan Yulin shekarar nan.