Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP karkashin jagorancin Rabi’u Kwankwaso, ta ce ba ta manta da karfin jam’iyyar PDP da APC ba, sai dai tana shirye shiryen ganin ta bada mamaki. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Laraba a Legas.
Alkali ya ce jam’iyyar NNPP za ta ba da mamaki a duk fadin kasar a babban zaben shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Zanga-Zanga Sun Tsayar Da Al-amura Cak A Afrika Ta Kudu
A cewarsa, irin shugabancin da jam’iyyar NNPP za ta kawo a Nijeriya zai sha bamban da yadda sauran jam’iyyun siyasa suka bayar da kuma yadda suke bayarwa a yanzu.
“Muna shirin rage ɓacin rai da fushi da takaici a cikin ƙasar nan.
“NNPP jam’iyya ce da ta samo asali daga yunkurin yan kasa wanda zai bada damar kawo da Najeriya ingantacciya
“Yanzu mun samu ‘yan takararmu a matakai daban-daban, kuma muna shirye-shiryen lokacin yakin neman zabe nan ba da dadewa ba.
“Hakika, ba mu manta da karfin abin da PDP da APC za su iya yi ba a zaben.
Jam’iyyar mu tana kan hanya. Muna da ƙarfi sosai. Muna kara karfi. Mun damu da makomar Najeriya da dimokuradiyyarmu.”
A WANI LABARI KUMA: Gwamnan Kano Yayi Alƙawarin Samar Da Karin Jami’o’i Biyu A Jihar
Gwamnati jihar kano ta yi alkawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin Kara bada damar inganta Ilimin matasa a jihar.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi, yayin bude taron makon matasa wanda Majalisar dinkin duniya ta ware domin duba kan matsalolin matasa da Kuma lalubo hanyoyin da za’a magancesu.