Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da ke neman mukaman siyasa a zabe mai zuwa na shekarar 2023 da su yi murabus daga mukamansu.
Umurnin na Gwamna jihar ya ce “An ba su daga yanzu zuwa ranar Litinin, 18 ga Afrilu, 2022, su yi murabus.”
Wannan ya yi daidai da sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.
Wasu kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman da ma sakataren gwamnatin jihar, duk sun fito takara a ofisoshi daban-daban na zaben shekarar 2023..
Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa tashin hankali ya dabaibaye da dama daga cikin wadanda ke ficewa daga Gwamnati, tare da rashin tabbas kan abin da zai faru a babban zaben kasar nan dake tafe.
A wani labarin Kuma na daban.
Tikitin takarar Shugaban kasa: Ko an bani tikiti, ko ba a bani ba, bazan taba ficewa daga Jam’iyar PDP ba——- Nyesom Wike
Gwamnan jihar Ribas kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Mista Nyesom Wike, ya ce zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar PDP, ko da kuwa bai samu tikitin takarar shugaban kasa ba.
Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP reshen jihar Neja a sakatariyar jam’iyyar da ke Minna a ranar Asabar.
Gwamnan ya ce babu laifi dan takarar da aka amince da shi idan aka dogara da adalci da gaskiya.
Yayin da yake neman goyon bayan masu ruwa da tsaki ya ce shi ne dan takara daya tilo da zai iya kayar da jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023.
“Na zo yau ne domin in shaida muku cewa na ba da kaina na tsaya takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyarmu ta PDP, tun 1988 ina jam’iyyar PDP, ban taba ficewa daga jam’iyyar ba, kuma ba zai taba barin jam’iyar ba.
Ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro da ake fama da su a kasar nan, inda ya yi zargin cewa gwamnati mai ci ba ta Samar da isasshen tsaron rayuka da dukiyoyin al’uma ba.