Gwamnonin jam’iyyar APC guda tara, sun yi wata ganawar sirri ta sa’a daya da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Daura.
A yayin ganawar ne kuma suka bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim.
Shettima ya kasance yanzu shine a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, a zaben 2023.
Gwamnonin sun kuma ce sun amince da hadakar Tinubu da Shettima domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa.
Shugaban kungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC, Abubakar Bagudu, ya shaida wa manema labarai a karshen taron sirrin cewa:
“Mun yi matukar mamakin yadda Asiwaju Ahmed Tinubu ya bayyana a Daura ranar Lahadi cewa Sanata Kashim Ibrahim Shettima ne dan takarar mataimakin shugaban kasa.
Babu shakka, Sanata Shettima zai cika kyawawan halayen Asiwaju Tinubu, don haka Muna matukar farin ciki da zabin.
Su biyun za su sadu da juna kuma tabbas za su karfafa kan nasarorin da aka samu, Bagudu ya ce sun kaiwa shugaban kasa ziyarar ne a Daura domin taya shugaban kasar murnar Sallah.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, shi ma ya ce zabin Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa shawara ce ta gamayya da dukkanin gwamnonin masu ci gaba suka yi, inda ya kara da cewa dukkanin gwamnonin za su yi aiki tukuru don ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben 2023.
Gwamnoni taran sun haɗar: Aminu Masari (Katsina); Abdullahi Ganduje (Kano); Abubakar Bagudu (Kebbi); Abubakar Bello (Niger); Abdullahi Sule (Nasarawa); Hope Uzodimma (Imo); Kayode Fayemi (Ekiti); Simon Lalong (Plateau); da Nasir El-Rufai (Kaduna).