Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana shirinta na gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi ranar Asabar.
Hukumar ta kuma dage kan cewa mambobin dake hidimar kasa ne, kawai za su gudanar da tsarin tantance masu kada kuri’a ta hanyar amfani da na’urar BVAS a lokacin zaben. Vanguard ta tawaito.
KU KARANTA: Dattawan Arewa Sun Musanta Zaɓar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Su
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a karshen mako a lokacin da ya kai ziyara cibiyar taron kasa da kasa ICC.
INEC za ta gudanar da ayyuka uku a cibiyar da suka hada da sanar da wadanda suka yi nasara, gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa; da kuma zababbun Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai.
Ya bayyana cewa ‘yan takarar shugaban kasa da suka hada da Bola Tinubu na jam’iyyar APC; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na jam’iyyar Labour Party LP, da sauran su za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu.
Yakubu ya kuma bayar da tabbacin cewa karancin Naira a halin yanzu ba zai haifar da barazana ga gudanar da zaben ba saboda hukumar ta samu kwakkwaran tabbaci daga babban bankin Najeriya CBN cewa za a samar mata da kudaden da take bukata.
A wani labarin kuma: EFCC Ta Kwato Naira Miliyan 900 Na Shirin NHIS
Hukumar EFCC ta ce ta kwato karin kudi har Naira miliyan 900 na shirin inshorar lafiya ta kasa.
Kakakin hukumar Mista Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar.