Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta fitar da bayanan ‘yan takarar da jam’iyyun dà suka tsaua tsayar a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a dukkan mazabun kasar nan a ranar Juma’a.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wajen rantsar da sabuwar hukumar zabe ta mazauni gida (REC), Dokta Hale Longpet, ranar Alhamis a shedikwatar hukumar da ke Abuja.
Yakubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su binciki bayanai tare da neman maganin shari’a kan duk wani abu da aka gani ya saba wa doka.
“Yayin da muke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zabe na 2023, a gobe Juma’a 22 ga watan Yuli, hukumar za ta fitar da bayanan ‘yan takara da jam’iyyun siyasar da suka tsayar a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a dukkan mazabun kasar nan kamar yadda doka ta tanada.
“Ina kira ga daukacin ‘yan Najeriya (‘yan kasa da masu son tsayawa takara) da su yi amfani da damar da suka samu wajen bin diddigin bayanan ‘yan takarar da kuma neman hanyar shari’a kan duk wani abin da aka gani ya saba wa doka kamar yadda yake a sashe na 29 na dokar zabe ta 2022,” in ji shi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban hukumar ta INEC ya yi Allah wadai da yawaitar kararrakin da ake yi a kasar kafin zabe, inda ya ce ya zuwa yanzu INEC ta shiga cikin kararraki 334 a kan batutuwan da suka shafi tunkarar zaben 2023 a fadin kasar nan.
“Tuni, Hukumar ta cika da yawan shari’o’in da suka taso a gabanin zaben da suka taso daga yadda jam’iyyun siyasa suka gudanar da zaben fidda gwani na zaben 2023.
“Ya zuwa yanzu, an shigar da kararraki guda 334 gabanin zabe a sassa daban-daban na babban kotun tarayya a fadin kasar nan ta hanyar masu neman takara da ke kalubalantar zaben ‘yan takara ko kuma cire su daga jerin sunayen da aka mika wa Hukumar.
“Duk da cewa wadannan batutuwa ne kawai na cikin jam’iyya, amma duk wadannan shari’o’in an hade da Hukumar.
“Tare da fitowar bayanan sirri na ‘yan takarar gwamna da na mataimakin gwamna da kuma zabukan ‘yan majalisar jiha gobe, muna sa ran adadin ya karu fiye da haka,” in ji Yakubu.
Ya ce abin bakin ciki shi ne batun dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyun siyasa ya ci gaba da zama mai zafi a harkokin zaben Najeriya.
Ya yi alkawarin cewa INEC za ta ci gaba da yin cudanya da jam’iyyun siyasa tare da tsayawa tsayin daka kan duk wani laifi ta hanyar aiwatar da tanade-tanaden doka da tsaffin dokoki da ka’idoji.
(NAN)