Wakilan jam’iyyun siyasa a jihar Kaduna sun jajirce wajen ganin an gudanar da zabe cikin lumana a zabe mai zuwa, ba tare da tsokana da cin mutuncin juna ba da ka iya haifar da tashin hankali ba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A wata yarjejeniyar zaman lafiya da wakilan jam’iyyun siyasa 11 suka sanya wa hannu a zaben da za a yi a Kaduna ranar Laraba, jam’iyyun siyasar sun yi alkawarin cewa, “Mun yi alkawarin gudanar da zabe cikin lumana, ba tare da tayar da hankali da cin mutuncin jam’iyyun da ke adawa da juna ba, wadanda za su iya haifar da tashin hankali.
KU KARANTA: Sam Emefele Bai Cancanci Zama Gwamnan CBN Ba – Inji Wani Gwamna
Har ila yau, sun kuduri aniyar amincewa da sakamakon zabukan, muddin aka gudanar da shi cikin gaskiya da rikon amana tare da amincewa da yin amfani da tattaunawa mai ma’ana a matsayin hanyar warware matsalolin da ke tsakaninsu.
Sun kuma amince da yin aiki da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an hukunta da masu aikata laifuka yadda ya kamata kamar yadda dokokin zaben Najeriya suka tanada.
A wani labari kuma, Jihar Kebbi: Jam’iyar SDP Ta Narke A APC
Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar Kebbi, Alhaji Atiku Mai-Ahu; mataimakin dan takarar gwamnan, Barista Nafi’u Abubakar; da daukacin ’ya’yan jam’iyyar a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu, sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC. Kamar yadda Daily Psot ta ruwaito
A cewar wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na fadar gwamnati, Kwamared Abubakar Muazu Dakingari, dukkanin ‘yan takarar sanata na jam’iyyar SDP, da na majalisar wakilai, sai dan takara daya, da ‘yan takarar majalisar dokokin jihar duk sun sauya sheka.