Jam’iyyun siyasa 14 ne suka tsayar da ‘yan takara a zaben gwamna a jihar Kano a shekarar 2023.
An fitar da jerin sunayen jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu a hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta jihar Kano.
An kuma nuna jerin sunayen ‘yan takarar mataimakin gwamna, wanda ya yi daidai da yadda dokar zabe ta tanada.
An kuma fitar da jadawalin ‘yan takarar majalisar dokokin jihar a ofisoshin INEC da ke kowace mazaba 40 da ke jihar.
Jam’iyyun siyasar sun hada da APC, PDP, NNPP, PRP, APP, da ZLP, da sauran su.
Aishatu Mahmud ta jam’iyyar NRP ita ce mace tilo da ta tsaya takarar kujerar gwamna, yayin da Fatima Muhammad ta kasance mataimakiyar ‘yar takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Action Alliance (AA).
Malamin addinin musuluncin nan na Kano, Sheikh Ibrahim Khalil yana cikin ‘yan takarar gwamna.
Yana takara ne a karkashin jam’iyyar (ADC).
Haka kuma mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Nasiru Yusuf-Gawuna, shi ne dan takarar jam’iyyar APC, yayin da Alhaji Abba Kabir-Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba Gida-gida”, ke tsayawa takara a jam’iyyar (NNPP).
JARIDAR DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa sunan Sadiq Wali ya fito a jerin sunayen a matsayin dan takarar PDP, maimakon Mohammed Abacha, wanda a baya hukumar ta bayyana a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Da yake mayar da martani kan batun, jami’in hulda da jama’a na INEC, Mista Adam Ahmad-Maulud, ya ce aikin INEC shi ne kula da yadda za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyya.