Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya kalubalanci ‘yan Najeriya musamman matasa da su ba da fifiko tare da bayar da himma wajen karbar katin zabe na dindindin domin su samu damar shiga kada kuri’ar shugabanninsu a zabe mai zuwa.
Diri ya tabbatar da cewa katin zabe na PVC ya fi bindigar nan mai hatsarin gaske AK-47 karfi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Mambobin APC Sama Da 1,000 Sun Fice Daga Jam’iyar A Jihar Kogi, Sun Koma PDP
Ya ce “Ya kamata ‘yan Najeriya su shirya da PVCs. Shugabanci na yanzu ya ziyarci kasar nan da yunwa, fatara, tabarbarewar tattalin arziki da kuma barnatar da rayuka da dukiyoyin da babu gaira ba dalili.
“Al’ummar kasar nan su ne kadai ke da mafita ga duk wadannan. Ina kira gare su da su ‘yantar da kansu daga kangin da ake ciki a yanzu, domin katin zabe na PVC ya fi bindigar AK-47 karfi. Saboda katin zabe na PVC shine komai”.
Sanata Diri ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake jawabi a wajen taron bikin ranar Dimokuradiyya ta ba na a fadar Sarkin Glory Chapel da ke gidan gwamnati a Yenagoa.
Gwamnan ya kuma umarci masu rike da mukamai da su rika kallon kan su a matsayin bayi yayin da mutanen da suka ba su wannan mukami a matsayin ubangidan su da suke yi musu hisabi.
Ya kuma bayyana cewa ya kamata ma’aikatan da aka zaba ko aka nada su dauki irin wadannan mukamai a matsayin wata gata da kuma wani dandali na inganta rayuwar al’umma.
Kalamaina: “Yau kasancewar ranar Dimokuradiyya, ya kamata a tunatar da mu mu ci gaba da yi wa mutanenmu hidima. Idan an zabe ku ko aka nada ku a manyan ofisoshi da mukamai na gwamnati, ku lura cewa gata ce kawai.
“A duk ayyukanmu, mu sani cewa wadanda suka ba mu ikon yi musu hidima, iyayenmu ne kuma mu bayin su ne. Idan kuka mai da kanku abin bautawa, yaudarar kanku kuke yi kawai.”
Da yake tsokaci kan harin da aka kai cocin St. Francis Catholic da ke Owo, jihar Ondo, Sanata Diri ya sake jajantawa gwamnati da al’ummar jihar kan lamarin.
Ya ce gwamnatin Bayelsa tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Ondo sun bayyana cewa ba za a yi bikin ranar dimokradiyya ba.
Da yake bayyana Bayelsa a matsayin jiha mai zaman lafiya, Gwamna Diri ya ce an sake fasalin tsarin tsaro na jihar tare da sanya hannu kan dokar kare hakkin jama’a ta jihar Bayelsa domin kara kaimi ga kokarin hukumomin tsaro daban-daban a jihar.
A cewarsa, sama da matasa 5,000 ne rundunar sojojin karkashin jagorancin Brig-Gen. Eric Angaye (mai ritaya) kuma ya horar da su ta kowane fanni na tsaro don dakile ayyukan muggan laifuka.
Ya yi bayanin cewa an shigar da wasu kayyakin tsaro na jihar Bayelsa Vigilante da Bayelsa Volunteers a cikin rundunar kuma za a horar da ma’aikatansu don kara musu inganci.
Comments 1