Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bukaci yan Najeriya da su ziyarci hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Kasa watau INEC domin yin rajistan katin Zabe da zai ba su damar kada kuri’ar su a babban zaben shekarar 2023 Mai zuwa.
Bello ya bayyana cewa rajistan katin Zabe shi ne hanya daya tilo da mutane zasu sami damar amfani da yan’cin su da kuma ikon da kundun tsarin mulkin kasa ya basu, domin sauke hakkokin su amatsayin su na yan kasa Najeriya.
Kazalika Gwamnan ya yi kira ga daukacin matasan dake fadin kasar nan, da su shirya karban ragamar jagoranci ƙasar nan a zaben shekarar 2023, “Saboda lakacin su ne” inji Yahaya Bello.
A wani labarin Kuma na daban
Rundunar Sojin Ƙasa ta gudanar da Atisayen Harbin Bindiga a Jahar Katsina
Rundunar Sojin Ƙasa ta Bariki na 17 na Natsinta a ranar Laraba tayi kira ga ƙauyukan dake maƙwabtaka da Natsinta a Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jahar Katsina, da kada su tsorota a ranar Juma’a, idan Dakaru na 3 na Barikin suna gudanar da shirin koyon Harbin Bindiga.
Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Jami’in Hulɗa da Jama’a na Bariki na 17 Lt. SO Tamuno ya bayyana cewa shirin Harbin bindigar na daga cikin horswar Soji da ake yi akai-akai.
“Manufar shirin koyon harbin shine, a tabbatar da ƙwarewa da inganci a tsakanin Jami’an Soji.
“Haka zalika, yana da nufin inganta Makaman Dakarun Sojin a gasar Bariki-Bariki da za’a ga masu muƙamin Kofural da abinda yayi ƙasa.
“Wannan shirin koyon harbin ya wakana a ranar Juma’a 18 ga watan Maris na Shekarar 2022, wanda ya ƙunshi harba lafiyayyan Harsashi.
“Za’a ɗauki matakan da suka dace, tare da tabbatar dasu a lokacin domin tabbatar da samun nasarar gudanar da shirin harbin.
“Mazauna ƙauyukan Natsinta, da Masu Kiwo da Manoma ana shawartar su da su yi nesa da inda ake gudanar da harbin.
“Haka zalika, ana kira ga Al’umma da kada su razana a lokacin da suka ga gittawar Dakarun Sojin, da ƙarar bindiga a wurin da aka ware domin gudanar dashi,” inji Tamuno