Wata kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje mai goyon bayan Asiwaju wato NDA, ta ce tana goyon bayan tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Bola Tinubu domin ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023, wanda ta ce akwai bukatar sauran al’umma su bata hadin kai.
Sun nemi da kowa da kowa ya goyi bayan Tinubu domin zama shugaban kasa a 2023 ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.
Dakta Akin Badeji, Darakta Janar na sabuwar kungiyar wacce aka kaddamar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka ba Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Juma’a a Abuja.
Badeji, jigo ne dai a jam’iyyar APC a Birtaniya, ya fadi hakan ne bayan kaddamar da kungiyar.
Ya ci gaba da cewa; “Tinubu ya yi fice a matsayin dan siyasa daya da mafi kyawun nagartar ayyuka domin ci gaba daga kyawawan ayyukan na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“NDA ƙungiya ce wacce take da zabi da aka kafa da nufin samar da goyon baya a cikin Ƙasashen waje da kuma tsawon faɗin Nijeriya domin shugabancin Tinubu a 2023,” in ji Badeji.
Ya ce kungiyar tana da hedikwata a Landan, da kuma ofishinta na kasa a Babban Birnin Tarayya Abuja, ya ce ba za ta taba hutawa ba har sai ta cimma burinta na ganin an zabi shugabancin Tinubu.