Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce halin da Najeriya ke ciki ya yi muni matuka, ta yadda kasar nan na bukatar zautacce da zai gyara al’amura.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a jihar Kogi a ranar Laraba.
Wike ya yi kira ga wakilan da su zabe shi a zaben fidda gwani na jam’iyar, inda ya ce yana da abin da ya kamata ya tafiyar da mulkin Najeriya da kuma kai ta tudun muntsira.
“abubuwan da nakeson cimmawa sun yi ya yawa. Ina so in yi amfani da makamashi don yi wa kasa aiki,” in ji shi
“Na bayar da kaina ga jam’iyyata, kuma a zabe ni in zama shugaban Tarayyar Najeriya. A tarihin kasar nan ba a taba samun rabuwar kai irin haka ba. Zan iya dawo da kasar bisa tafarkin da ya dace. Ba tare da la’akari daga ina Mutum ya fito ba. Ana bukatar zautacce ya mulki Najeriya,” inji shi.
Ya ce ’yan Najeriya na bukatar mutum marar tsoro da jajircewa irinsa wanda zai iya fadin gaskiya a fannin mulki.
Ya kuma yi kira ga wakilan da kada su yi shakkar sahihancin sa wajen inganta tattalin arzikin kasar.
“Amma ni, idan ba ku zabe ni a zaben fidda gwani na jam’iyyarmu ba, zan ci gaba da zama dan PDP. Na ci gajiyar wannan jam’iyya, don haka ba ni da wani uzuri da zan bayar, na sauya sheka zuwa wata jam’iyya,” inji shi.
Dan takarar shugaban kasa ya yi fatali da wadanda suka juya wa PDP baya bayan sun ci gajiyar jam’iyyar.
A nasu jawabin, tsoffin gwamnonin jihar biyu, Ibrahim Idris da Captain Idris Wada, ciki har da shugabannin majalissar zartaswar jam’iyyar na jihar, sun yaba da kyawawan halaye na gwamna Wike, tare da ba shi tabbacin goyon bayansu a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar da aka shirya yi a karshen watan nan.
Comments 1