Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci wakilan jam’iyyar APC da su yi nazari mai ma’ana wajen zabar ‘yan takara a zaɓen fid- da-gwani na jam’iyyar da ke tafe.
A wata sanarwa mai d’auke da sa hannun babban mai taimakawa mataimakin shugaban kasa kan kafafan yada labarai, Laolu Akande ya fitar, tace Osinbajo ya gana da wakilan jam’iyyar APC na jihohin Osun da Imo da kuma Kogi.
Ziyarar tasa wani bangare ne, na cigaba da ziyarar neman kuri’un wakilan jam’iyyar a fa’din kasa Najeriya, kuma kawo yanzu ya ziyarci jihohi da dama cikin 36 da ake da su.
A ziyarar da ya kai Osogbo, babban birnin jihar Osun, ya samu kyakkyawar tarba daga al’ummar jihar tare da samun goyan baya daga Ataoja na Osogbo, Oba jimoh Oyetunji Olanipekun, Larooye na biyu, wanda ya bayyana Osinbajo a matsayin shugaba mai jiran gado bisa cancanta.
Sanarwar ta k’ara da cewa a jihar Imo, nan ma ya samu sukunin ganawa da wakilan, inda ya basu tabbacin cigaba da kawo ayyukan alkhairi a jihar.
Mataimakin shugaban kasar, ya kuma gana da wakilan jam’iyyar APC na jihar Kogi a birnin Abuja, inda aka gabatar da tambayoyi da kuma amsoshi kan kamun ludayin jam’iyyar APC, yana mai bada tabbacin inganta harkokin tattalin arziki a kasa baki d’aya.