Jam’iyyar adawa ta PDP ta doke jam’iyyar APC a daya daga cikin rumfunan zabe da ke gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim, Kaduna a zaben gwamna da aka yi ranar Asabar Punch ta rawaito.
Dan takarar babbar jam’iyyar adawa, Isa Ashiru Kudan, ya lashe rumfar zabe mai lamba 014 da kuri’u 77 yayin da Uba Sani na APC ya samu kuri’u 40.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Lallasa Yar Takarar Mataimakiyar Gwamna a Akwatinta Da Kuri’u Masu Yawa
Shugaban hukumar Mohammed Baso, wanda ya bayyana sakamakon, ya ce jam’iyyar Labour ta samu kuri’a 0. PRP 1, NNPP 1 yayin da aka samu kuri’u 7 da ba su da inganci.
A wani labarin kuma, Hukumar Zabe INEC Ta Dage Zabe A Wasu Rumfuna 10 Na Legas
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da ake yi a ranar Asabar a rumfunan zabe 10 da ke unguwar Victoria Garden City (VGC) da ke kewayen yankin Lekki na jihar.
Kwamishinan Zabe na INEC, Segun Agbaje ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai a dakin taro na VGC.
A cewarsa, tawagar da aka tura a matsayin ma’aikatan wucin gadi a ranar Asabar din nan sun yi shakkun shiga rukunin gidajen VGC saboda zargin cewa an yi garkuwa da su ne a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Agbaje ya ce jami’an wucin gadi na hukumar sun kafa kayan zabe a gaban gidan a ranar Asabar amma mazauna yankin sun yi ikirarin cewa ‘yan banga na iya kawo cikas ga shirin, don haka ba su samu kwanciyar hankali ba kuma ba za su iya kada kuri’unsu ba.
Ya ce lamarin ke da wuya jami’an tsaro suka shawo kan lamarin don haka shi da tawagarsa suka bar yankin.