Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana tikitin tsayawa takarar musulmi da musulmi a matsayin yaudara, yana mai cewa abin da Najeriya ke bukata a 2023 gogaggen shugaba ne da zai iya hada kan al’umma. Kamar yadda Vanguard ta ruwaito
Ya ce Najeriya ba ta bukatar karamin dan siyasa a matsayin shugaban kasa, sai dai gogaggen dan siyasa da zai jagoranci ta a zaben 2023 mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Hana Gidajen Talabijin Din Kenya Yada Shirin Rantsar Da Ruto
Ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya su kawar da siyasar kabilanci a wannan karni na 21, kuma su hada kai a matsayin al’umma daya dunkulalliya domin ci gaban kasa.
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi kan babban zabe mai zuwa da kuma halin da al’ummar kasar nan ke ciki, Gumi ya ce babu laifi ‘yan siyasa sun yi takara sau da yawa, suna neman nasara.
Da yake jawabin kan Atiku Abubakar Gumi yace “Najeriya na bukatar gogaggen dan siyasa. Ba ma bukatar karamin dan siyasa ya zama Shugaban kasa. Halin da ake ciki a Najeriya a yau yana bukatar gogaggen dan siyasa don warware shi,” inji shi.
Agefe guda da yake tsokaci kan kan Tinubu wanda ya ce lokacin sa ne ya zama Shugaban kasa, Sheikh Gumi ya ce, “bai dace ba ya ce lokacin sa ne. Babu dalilin da zai ce lokaci na ne. Kar ku ce lokaci na ne domin idan mutane kamar ku za su zabe ku. Shi ma’aikaci ne nagari, zai iya yi. Tikitin tikitin Musulmi-Musulmi ba wajibi bane ba.”
“Dukkanmu mun sani, duk wadannan ‘yan siyasa suna neman kuri’u ne. Tikitin musulmi da musulmi shi ne, bari in yi amfani da harshen Hausa, wayo (yaudara). Ba addini ba ne. Ko zai yi aiki ko a’a, ba na son yin yaudara, amma akwai matsaloli da yawa. Hasali ma, dukkan jam’iyyun siyasa suna da nasu matsalolin. Tikitin Musulmi-Musulmi zai zama gwajin dakin gwaje-gwaje don wasu su yi koyi anan gaba ko a’a”.
Akan Peter Obi ya ce “matasan da ke biye da shi sun rabu kamar manya. Yana bukatar ya kai ga sauran sassan ’yan Najeriya. Dogaro ga matasa kadai ba zai wadatar da shi ba. Dole ne ya kasance a ko’ina, kuma kada ya bar siyasar zuwa yanki kadai daya”.
Sheikh Gumi ya yi gargadin cewa idan aka zabi dan siyasa maras gogewa a kan karagar mulki, zai yi wahala a iya yi wa al’umma aiki yadda ya kamata.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa ya dauki tsawon watanni shida, kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari yana nada Ministoci da jami’an gwamnati saboda shi (Buhari) dan siyasa ne maras gogewa.
Akarshe ya cigaba da cewa, rashin adalci da talauci ne ke haddasa rashin tsaro a kasar nan, inda ya kara da cewa shekaru bakwai na mulkin Shugaba Buhari kusan kowane dan Najeriya yana jin radadin kuncin rayuwa da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskata.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamna Bagudu Ya Baiwa Hukumar Hisba Naira Milliyan 100
Gwamnatin jihar Kebbi ta bai wa hukumar Hisba naira milliyan dari, domin cigaba da gudanar da ayyukanta na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar nan.
Gwamna Abubakar Bagudu ne ya bayyana hakan, a jiya lahadi wajen bikin cika shekara 20 da kafa hukumar.