Wani jigo a jam’iyyar APC, Olusegun Osoba, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Tinubu, ya na da cikakken ikon tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
“Asiwaju Bola Tinubu a matsayinsa na dan kasa yana da yancin gabatar da kansa, mu dama bamu da wani gwani. Samar da wani gwani yanzu zai iya tarwatsa duk wani shiri yanzu, amma Asiwaju Bola Tinubu yana da yancin fadi tashin tabbatar da burinsa,” a cewar sa.
Osoba, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Ogun, ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin talabijin a ranar Talata.
KARANTA WANNAN: Matsayar Gwamnatin Tarayya na sake sanya dokar kulle saboda COVID-19
Ya ce dole ne shiyyar Kudu maso Yamma ta hade kanta tare da dinke duk wata baraka domin ganin cewa ta samu tikitin takarar shugaban kasar a babban zaben 2023.
A cewar Olusegun Osoba, akwai wata yarjejeniyar mutuntawa da aka yi a jam’iyyar APC na cewar shiyyar Kudu ce za ta samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Jigon APCn, ya kuma yi nuni da cewa duk da akwai surutai masu yawa daga shiyyar Gabas, babu wanda ya tuntube shi ko wani jigon jam’iyar da ra’ayin tsyawa takarar shugaban kasa a 2023.
Cikakken labarin yana zuwa…