Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa wani mutum a fadar shugaban Najeriya yana goyon bayan Atiku Abubakar gabanin zaben 2023. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Tsohon mataimakin shugaban kasar dai shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP.
Wike ya rasa tikitin takaran a gare shi a watan Mayu bayan zaben fidda gwani, kuma ya ci gaba da dagewa cewa shugaban Jam’iyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya sauka daga kan mukaminsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugabancin Kasa 2023: Ina Fatan Tinubu, Ko Obi Ya Yi Nasara – Gwamna
A jawabinsa a harabar Ahoada na Jami’ar Jihar Ribas, ya ce wasu mukamai a jam’iyyar da shugaban Jam’iyar na kasa ya kamata su fito daga Arewa ne.
Gwamnan ya zargi bangaren Atiku da girman kai saboda suna ganin suna da goyon baya mai karfi.
A ranar Alhamis a taron majalisar zartaswa ta kasa karo na 97, Atiku ya bayyana kudurinsa na ganin an shawo kan rikicin.
Dan takarar na PDP ya kuma bayyana cewa sabani ya zama ruwan dare a tsakanin mambobin jam’iyar da sauran jam’iyyun siyasa.
A WANI LABARIN KUMA: Rufa’i Hanga Ya Gaji Takarar Shekarau A Jam’iyyar NNPP
Sanata Rufa’i Sani Hanga ya lashe tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar NNPP.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Hanga ya samu tikitin ne wanda Sanata Ibrahim Shekarau ya janye daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP.