By Abbas Yakubu Yaura
Tauraruwa gwamna Yahaya Bello na jihar kogi na son tsayawa takarar shugabancin kasa a babban zaben shekarar 2023 dake tafe sai kara haskawa take a idon jama’ar dake fadin Najeriya.
Wanda hakan yasa wasu kungiyoyin suke ta kiraye kirayen daya tsaya takarar shugabancin kasa a babban zaben mai zuwa kamar yadda kungiyar Mata ta (Mammoth) tafito tare dayin dafifi a birnin tarayya Abuja don nuna goyan bayan su a gareshi inda suke cewa da a bayyana shi a matsayin dan takarar shugabancin kasa.
Kungiyar matan wadanda suka fito a karkashin inuwar kungiyar (WUYABEL) bayan tattakin hadin-kan da suka yi, mai taken “Mata Miliyan Daya ga Yahaya Bello” don nuna goyan baya su. A yayin tattakin sun bayyana cewa idan akayi la’akari da da irin farin jinin da yake dashi da kuma irin yadda yake tafiyar da mulkin jama’ar jihar sa ya isa ayaba masa duba da kwarewar da yake da ita.
Kazalika sun ce hazakar sa da kwarewar sa tasa Al’ummar Najeriya ke fatan ya tsaya takara dan kawo musu dauki tare da fitar dasu daga cikin halin da suke ciki wajen kaisu ga tudun muntsira.
Wannan dai ba shine karon farko da wasu kungiyoyin suke neman Yahaya Bello daya tsaya takarar shugabancin kasa ba a babban zaben dake tafe.