Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka kan harkokin da suka shafi Afirka, Molly Phee, a ranar Talata, ya ce akwai bukatar a ilimantar da ‘yan Najeriya kan tsarin zabe.
Phee ya ba da wannan shawarar ne a yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja.
KU KARANTA: Zanga-zanga Ta Barke A Ogun Kan Karancin Sabbin Takardun Naira
Mataimakin Sakatare na Amurka ya yi tsokaci game da sashe na 134 (2) na dokar zabe wanda ke bayyana yadda shugaban kasa zai iya fitowa da kuma yanayin da ka iya haifar da zabe na biyu.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2022, kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Festus Okoye, ya bayyana cewa:
Sashe na 134 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, wanda shine tushen dokar kasa, ya ce ya zama wajibi kafin a ce an zabe kowa a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya, dole ne dan takarar ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada a zaben.
Ba iya haka ba sai Kuma ya samu kashi hudu na kuri’un da aka kada kashi biyu bisa uku na Jihohin Tarayya da Babban Birnin Tarayya.
Phee, wanda ya bayyana kwarin gwiwa ga INEC ta gudanar da sahihin zabe, ya bayyana cewa, idan aka ilimantar da masu kada kuri’a game da dokar zabe, zai taimaka wajen mika mulki cikin lumana.
A wani labarin kuma: FG Ta Amince Da Ɗaga Likkafar Wata Kwaleji A Kano Zuwa Jami’a
Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a ranar Talata ta amince tare da daukaka Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso zuwa Jami’ar Ilimi.
Sakataren zartarwa na hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, a lokacin da yake mika lasisin aiki ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a Abuja, ya ce jami’ar an amince da ita a matsayin jami’a ta 61 a fadin kasar nan.