An samu tashin hankali a karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra a ranar Talata yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ne suka yi Batakashu da jami’an rundunar ‘yan sanda, har na sama da sa’o’i uku a mahadar Osumoghu, a lokacin da ake gudanar da zaben Gwamna a jihar.
Hakan ya tilastawa jami’an tsaro na hadin gwiwa datse mahadar Osumoghu da ke kan iyaka da jihar Imo.
Wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa, wadanda ake zargin masu fafutukar kafa kasar Biafra ne da nufin kawo cikas a zaben jihar Anambra.
A lokacin da daya daga cikin wakilin jaridar PUNCH da ke sa ido a zaben da ake gudanar a Ihiala ya shiga rudani da har ya kutsa Kai cikin jami’an tsaro, sun umarce shi da ya bar wurin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ta Tabbatar da Raunin Pogba
“Ka kaurawa Nan wurin. ‘Yan uwanku (wadanda ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne) sun shafe sama da sa’o’i uku a nan Muna Bata kashi.”
“Wasu daga cikinsu har yanzu suna cikin dajin. Kawai kunemi hanyar da zaku bar Nan, donmin kare lafiyar ku, ”in ji wani dan sanda.
Kazalika wannan Batakashu ya Sanya mazauna yankin kauracewa yankin baki daya..
Comments 1