Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana Mista Mayokun Lawson-Alade a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabar Akure ta Arewa ta Kudu na jihar Ondo.
A cewar INEC, Lawson-Alade na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 26,379 inda ya doke Mista Olumuyiwa Adu na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 24,201.
Jami’i mai kula da zaben na INEC, Farfesa Deji Ogunseni na Jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Akure, FUTA ne ya sanar da sakamakon zaben a hedikwatar hukumar a ranar Lahadi da safe.
A wani labarin Kuma na daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wata yarinya ‘yar shekara 18 mai suna Blessing John, a lokacin da take neman matsafi domin siyan wani yaro da ta yi garkuwa da shi.
Yaron (wanda aka sakaya sunansa) daga unguwarsu dake Michika ta kai shi zuwa garin Mubi don neman mai siya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan sirri.
Nguroje ya ce matashiyar ta shaida wa ‘yan sanda masu binciken cewa ta sace yaron ne domin ta samu kudi don siyan mota da yin rayuwa mai dadi.
“Ta kai yaron Mubi domin ta sayar, amma da ta kasa samun masu sayan a waya, sai ta yanke shawarar neman wani mai siyan.
Sai dai kuma tayi rashin sa’a a yayin data gama magana da wanda bai dace ba, shi kuma ya sanar da ‘yan sanda,” inji shi.
A cewarsa, matashiyar ta samu ganawa da wani mai garkuwa da mutane a ziyarar da ta kai garin Mubi a kwanakin baya, inda wata kawarta ta shaida mata cewa za ta iya samun kudi ta hanyar samar da ‘ya’ya ga masu tsafi da masu safarar mutane.
Kakakin ‘yan sandan ya yi kira ga iyaye da su rika kula da unguwanninsu tare da kai rahoton mutanen da ake zargi da motsin da basu yarda dashi ba zuwa ofishin tsaro mafi kusa.