By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyiorcha Ayu, ya gargadi ‘ya’yan jam’iyyar sa game da rigingimun cikin gida gabanin gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2022 da kuma sauran zabukan da zasu biyo baya.
Ayu ya yi wannan magana ne a ranar Litinin a hedkwatar jam’iyyar dake Abuja, yayin wata ganawar da ya yi da ‘yan takarar gwamnan jihar Ekiti su 17.
A taron wanda ya kasance na kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa, Ayu ya yi barazanar sanya takunkumi ga duk wani mai son tsayawa takara daya yi tazarce.
Yace, “Halin jam’iyyar shi ne na hadin kai hankalin jam’iyyar shi ne na jam’iyyar da za ta yi yaki tare a dunkulewa wuri guda, da fatan za a iya kwato jihohi da dama, da yawa daga cikin ‘yan majalisar tarayya, duka majalisun biyu, ko jiha dama Majalisun dokoki.
“Ba za mu shiga wani zabe don mu sha kaye ba. Za mu shiga kowane zabe da niyyar cin nasara kuma ina ganin ya kamata ya zama halin kowane dan jam’iyyar PDP.Ba wani muhimmanci gare mu a shugabancin jam’iyyar ko kuna son wani dan takara ko ba ku so.
“Da zarar jam’iyyar ta yanke shawara kan dan takarar, alhakin kowane dan gidan PDP ne ya yi wa wannan dan takara yakin saboda ba wai dan takarar ku kadai kuke yi ba, PDP kuke fada.
“Don haka, kuna da alhakin tallafa masa, Duk wanda ya yi akasin haka, za mu za a yi la’akari da shi a matsayin dan adawa da jam’iyya.
“Halin da PDP ke ciki a yau shi ne duk wanda ke adawa da PDP ba zai yi tafiyarsa kawai ba saboda bama son ‘ya’yan jam’iyyar mu suna fada da ‘ya’yan jam’iyyar.”
Ayu yace jam’iyyar ta fadi zabe a baya saboda an raba kan shugabannin a jihohi daban-daban da mabiya.
Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da Gwamna Nyesom Wike na Rivers, sai Okezie Ikpeazu Abia, Seyi Makinde na Oyo da kuma Samuel Ortom na jihar (Benue).