Hukumar tsaro ta Civil defence a Najeriya ta sanar da kaddamar da lambar kira kyauta, matakin da ta ce na da nufin dakile tabarbarewar tsaro da kuma dakile tashe-tashen hankulan a lokacin zaben gwamnan jihar Ekiti.
Hukumar INEC dai ta sanar da sanya gobe Asabar 18 ga watan Yuni 2022 domin gudanar da zaben Gwamnan jihar ta Ekiti.
Rundunar ta kuma ce ta kafa wani dakin karbar bayanai a hedikwatar Rundunar ta Jiha tare da tallafi daga Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka, da tallafin Burtaniya.
Bayanin Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na hukumar NSCDC, DCC Olusola Odumosu, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wani bangare na dabarun tabbatar da ingantaccen sa ido kan harkokin tsaro a ranar 18 ga watan Yuni, zaben gwamna a jihar Ekiti, jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence na Najeriya sun kafa dakin kula da halin da ake ciki.
Mukaddashin babban kwamandan rundunar ‘yan sanda mai kula da ayyukan zaben jihar Ekiti, Haruna Muhammed, fdc, ya ce duk da cewa jihar ta samu isasshen tsaro, amma yana da kyau a tabbatar da hakkin mata da sauran marasa galihu kafin nan.