By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta gargadi jama’a da cewa duk wani tashin hankali na ‘yan daba a yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, a jihar da aka shirya yi ranar Juma’a, ba za a amince da shi ba.
Rundunar a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jihar, DSP Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, ta ce rundunar tare da sauran jami’an tsaro a jihar sun shirya tsaf yayin gudanar da zaben fidda gwani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A bisa la’akari da zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC mai zuwa a jihar Neja da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Mayu, 2022, rundunar ‘yan sandan jihar na son sanar da jama’a da jiga-jigan jam’iyyar, cewa rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro a jihar sun samar da isassun matakan tsaro kafin, lokacin da kuma bayan lokacin atisayen”.
“Rundunar ta kuma yi gargadin cewa duk wanda bai da wata alaka da atisayen na zaben fidda gwani to ya nisanci wurin da za a gudanar da atisayen.
Haka nan kuma ana shawartar dukkan wakilan da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin rundunar a shirye take kuma ba za ta lamunci duk wani tashin hankali da ayyukan ‘yan daba ba. “.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen dakile duk wani bata-gari da ke son yin amfani da irin wannan hanya wajen tada fitina a lokacin atisayen gudanar da zaben fidda gwani.
Sai dai ta shawarci iyaye da masu kula da su da su rinka yin galaba a unguwanninsu don kada a yi amfani da su a matsayin ’yan bangar siyasa wajen kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a da harkokin siyasa, domin duk wanda aka samu da laifin damfarar jama’a za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.