By Abbas Yakubu Yaura
Shahararriyar ‘yar gwagwarmayar zamantakewa da siyasa a shafukan sada zumunta, Aisha Yesufu, ta caccaki mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, inda ta bayyana shi a matsayin mai cin amana.
Sai dai ta bayyana cewa a zahiri Osinbajo bai ci amanar tsohon ubangidansa kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ba, amma yaci amanar ‘yan Najeriya ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sai Na Yiwa Atiku, Tinubu Murabus Daga Harkokin Siyasa — moghalu Alfahari
Tinubu, ya samu kuri’u 1,271 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Rotimi Amaechi, wanda ya samu kuri’u 316. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya zo na uku ne kawai a zaben fidda gwani, inda ya samu kuri’u 235.
A’isha ta ba da shawarar cewa Mataimakin Shugaban kasa, wanda da yawa daga cikin jama’ar Kudu maso Yamma ke kallon cewa ya ci amanar takarar shugaban kasa da ya yi takara da tsohon ubangidansa, ya gaza ne saboda wai ya juya wa jama’a baya.
Ta yi ikirarin cewa ‘yan Najeriya da dama ne suka zabi jam’iyyar APC a shekarar 2015 kawai saboda fuskar Osinbajo a kan fastocin yakin neman zabe amma ya gaza.
Aisha ta wallafa a shafinta na Twitter cewa: “Osinbajo @ProfOsinbajo ya ci amanar jama’a ba Tinubu ba. Da yawa sun zabi tikitin jam’iyyar APC a shekarar 2015 saboda Osinbajo.
“Ya shiga can ya juya wa mutane baya. Ya yanke shawarar ya goyi bayan zalunci da danniya!”
Comments 1