Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wadanda suka kada kuri’a a jam’iyyar APC a zaben fidda gwani na shugaban kasa yanzu haka suna yin nadamar shawarar da suka yanke.
Amaechi ya ce wakilan da suka bari kudi suka yi tasiri a kan shawarar da suka yanke a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa yanzu haka suna nadama.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-ogun-ta-ayyana-ranar-talata-a-matsayin-hutu-don-yin-rijistar-katin-zabe/
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 60 da haihuwa na Apostle Eugene Ogu, Janar Overseer na Abundant Life Evangel Mission, a karshen mako a garin Fatakwal na jihar Ribas.
Ya yi nuni da cewa sanya kudi don samun kuri’u ba zai magance matsalolin Najeriya ba.
Amaechi ya kuma bukaci bayin Allah da su yi wa talakawan Najeriya addu’a domin su zabi shugaban da zai magance matsalolin kasar.
A cewar Amaechi: “Wadanda suka kada kuri’a a zaben fidda gwani na APC, su waye? Su talakawan Najeriya ne. Kudaden da suka samu sun warware musu matsalar nan take, yanzu suna cewa sun yi kuskure, yanzu kuna jin abubuwa daban-daban.
“Idan kuna yi mana addu’a, ga shugabancin kasar nan, amma kuma ku yi wa talakawan Najeriya addu’a domin su zabi shugaban da ya dace ya shugabanci kasar nan.
“Ba da kudi ba shine mafita ga matsalar Najeriya ba. Maganin matsalar Najeriya ita ce dukkan ku dole ne ku tashi.”
A yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja, Amaechi ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar, Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya zo na biyu bayan Tinubu wanda ya samu mafi yawan kuri’u.
Rahotanni sun bayyana cewa zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya barke ne sakamakon sayen kuri’u.