musa wada

Zaben Gwamna A Kogi: Zan Garzayan Kotu-Dan Takarar PDP

Dan takarar gwamna a jihar Kogi a jam’iyyar PDP, Musa Wada ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta fitar.

Da yake yiwa manema labarai bayani a garin Lokoja a ranar Lahadi, Musa Wada ya yi zargin cewa  sakamakon zaben na boge ne aka fitar domin ayyana Yahaya Bello na APC a matsayin gwamnan jihar.

Har wala yau ya zargi APC da magudin zabe musamman a Kogi ta tsakiya wato inda gwamnan ya fito.

Ya yi alkawarin zuwa kotun sauraren kararrakin zabe domin kalubalantar sakamakon zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *