• Hukuma zabe Mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta maye gurbin sunan Soludo, da na Ozigbo a matsayin Wanda zai yi takarar gujerar gwamnan na jihar Anambra a inuwar jam’iyar APGA.
• Kazalika hukumar zaben ta ki wallafa sunan ko daya daga cikin yan takarar jam’iyar adawa ta PDP.
• Hukumar zaben dai ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar ne a ranar 6 ga watan Nuwan ban shekarar nan da muke ciki.
Hukumar zaben Mai zaman kanta ta kasa INEC, ta fitar da sunayen Yan takaran a zaben watan 6 ga watan Nuwanban shekarar nan, a hukumar ce, Wanda zai gudana ajihar Anambra, Amma ta ki sanha sunan Dan takarar jam’iyar APGA Farfesa Chukwuna Soludo. .
Kazalika daga cikin sunayen wadanda a ka cire akwai, Dan ta karan jam’iyar PDP Wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyar wato Valentine Ozigbo.
A maimakon sunan Farfesa Soludo, Hukumar zaben ta kasa, ta Sanya sunan Michael Umeoji a matsayin Dan takarar jam’iyar APGA, ya yin da haryanzu ake jiran tsammani, a kan hukuncin da Kotu za ta yanke, kan yan takarar jam’iyar adawa ta PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an yan sandan jihar Katsina sun kashe wani kasugumin Dan bindiga ta re da kubutar da wata mata
A bangaren jam’iya Mai Mulki ta APC kuwa, hukumar INEC ta wallafa sunan Emmanuel Andy Ubah, Wanda Kuma shine dan takara Mafi tsufa daga cikina Yan takarkarun, inda ya ke da shekara 62.
Comments 1