A ranar Larabar da ta gabata ce jam’iyyar PDP ta tantance ‘yan takara shida da ke neman tsayawa takarar gwamna a jihar Osun, wanda za’a kada kuri’a a ranar 16 ga watan Yulin shekarar nan
Kwamitin tantancewar yana karkashin jagorancin tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke.
Wadanda aka tantance sun hada da Sanata Ademola Adeleke, Dr Akin Ogunbiyi, Hon. Omirin Emmanuel Olusanya, Dele Adeleke, tsohon sakataren gwamnatin jihar Osun, Alhaji Abdulfatai Akinbade da Mista Dotun Babayemi.
Adoke ya ce kwamitin zai mika rahotonsa nan da sa’o’i 48 masu zuwa.
Ogunbiyi, Oluseye da Akinbade sun bayyana kwarin gwiwa kan yadda kwamitin tantancewar zai iya yin adalci.