…Jam’iyyar APC ta samu sama da Naira biliyan 1.3 daga sayar da fom din tsayawa takara ga ‘yan takarar jihohin.
Jam’iyyar APC mai mulki ta samu sama da Naira biliyan 1.3 daga sayar da fom din nuna sha’awar tsayawa takara ga ‘yan takarar gwamna a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Jam’iyyar APC ta yi cinikin fom din a kan Naira miliyan 50 sannan ta sayar da su a shedikwatarta ta kasa da ke Abuja tsakanin ranakun 15 zuwa 22 ga watan Fabrairu, kamar yadda jadawalin ayyukan da Sakataren shirye-shirye na kasa, Suleiman Argungu ya sanya wa hannu.
A jihar Kogi, da dama daga cikin masu neman kujerar sanatoci a shiyyar uku sun taso inda kowannen su ya yi alkawarin karfafa nasarorin da Gwamna Yahaya Bello ya samu.
KARANTA HAKANAN APC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takarar Gwamnan Jihar Kogi, Bayelsa Da Imo
Wadanda ke kallon kujerar Bello su ne Abdukareem Jamiu; Dr Sanusi Ohiare; James Faleke; Ahmed Ododo; Salami Deedat; Shuaibu Audu; Yakubu Oseni; Akanta Janar na jihar, Momoh Jibril; Yusuf Okala da kwamishinan kudi Ashiru Idris.
Sauran sun hada da Edward Onoja, Stephen Ocheni, Abubakar Achimugu, Idachaba Friday, Salaudeen Abdulkudus, David Jimoh, Sanata Smart Adeyemi, Muritala Ajaka da Halima Alfa.
A Bayelsa, wakilanmu sun ruwaito cewa Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva, Ogbomade Johnson, Joshua Maciver, Barista Daumiebi Sunday Festus, Farfesa (Mrs) Ongobi Maureen da kuma Lyon Pereworimini David ne ke takara.
A halin da ake ciki, akwai damuwa ga Sylva yayin da wasu masu ruwa da tsaki suka ce dole ne ya yi murabus kafin lokacin kada kuri’a.
Yayin da ake shirin gudanar da zaben Bayelsa a watan Nuwamba, masana sun ce Sylva na da isasshen lokacin yin murabus kafin lokacin kada kuri’a.
A Imo, Gwamna Hope Uzodimma na neman sake tsayawa takara a jam’iyyar APC. Hakazalika, wata ‘yar takara Juliet Awa Obasi za ta fafata da gwamnan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ba ta da sahihin ranar zaben fidda gwani har yanzu.
A cikin jaddawalin ayyukan zaben wanda sakataren kungiyar na kasa, Suleiman Argungu ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta sanya ranar 10 ga watan Afrilu domin gudanar da zaben fidda gwani.
A Wani Labarin Kuma Bankunan Sun Tabbatar Da Samun Karin Kuɗade, Suna Kuma Durawa A Injin ATM
Babban bankin kasa CBN ya saki wasu tsofaffin takardun kudi zuwa bankunan kasuwanci a daidai lokacin da babban bankin kasar ke kara zage damtse wajen cika tattalin arzikin kasar da karin makudan kudade bayan da aka dade ana fama da tabarbarewar kudi da ya janyo wa miliyoyin ‘yan Najeriya da mazauna kasar cikin wahala.
A ranar Alhamis ne CBN ya fara sakin biliyoyin Naira ga DMB. Jami’an bankin sun ce CBN ya sake sakin biliyoyin Naira ga masu ba da lamuni a ranar Juma’a