Hukumar zabe ta jihar Kaduna ta ayyana Mista Phillip Gwada na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin karamar hukumar Jaba ta jihar Kaduna.
Shugaban zaben, Farfesa Peter Omale shi ne ya ayyana Philip a ranar Litinin a ofishin zaben dake garin Kwoi.
Omale ya ce Gwada ya samu kuri’a 9,012 wanda ya sanya ya doke Mista Benjamin Jock na jam’iyyar APC wanda ke da kuri’a 5,640.
Ya kuma bayyana Alhamdu Gyet na jam’iyyar ADP a matsayin wanda ya zo na uku da kuri’a 2,732.
“Mista Phillip Gwada na jam’iyyar PDP, ya cika dukkanin dokoki kuma ya samu kuri’u mafi rinjaye, a don haka ina ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben”, inji Omale.