Dan takarar jam’iyar adawa ta PDP Mr Salasi Musa ya lashe zaben Karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.
Jami’in hukumar zabe Dakta Sanusi Gambo ne ya bayyana sakamakon zaben a safiyar yau Litinin, inda ya ce, Salasi Musa na jam’iyar PDP ya Sami kuri’u 19,402, yayin abokin hamaiyar sa na jam’iyar APC Sama’ila Leeman ya sami kuri’u 14,829.
Kazalika Jam’iyar PDP ce ta lashe kujeru 8 cikin 12 na mukaman Kansuloli a karamar hukumar Chikun, yayin da APC ta Sami kuri’u 4 kacal, kamar yadda Gambo ya bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar yan sand at horas da Jami’an Civilian JTF 312 a jihar Kaduna
Idan za’a iya tunawa Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Kaduna KAD-SIECOM, ta bayyana ranar 4 ga watan Satumban ne, a matsayin ranar da za’ayi zaben kananan hukumomin jihar Kaduna baki daya, inda daga bisani ta dage na wasu kananan hukumomi zuwa ranar 25 ga watan, bisa dalilan tsaro.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin jihar Oyo ta sanar da wasu mazauna yankin hadarin kamuwa da cutar a mai da gudawa, inda ta bukace su dasu ba da fifiko kan matakan kariya.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya, Dakta Ayoola Adebisi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka yi a gidan wasan kwaikwayo na shirya fina finai a ma’aikatar yada labarai, al’adu da yawon bude ido dake sakatariyar Agodi, Ibadan.
Sanarwar ta zo ne bayan barkewar cutar a mai da gudawa a wasu kananan hukumomi, wadanda suka hada da, Iddo, Akinyele da Irepo.
Adebisi ya tabbatarwa da jama’a shirye shiryen gwamnati don rigakafin barkewar cutar a mai da gudawa .Adebisi ya ce cutar amai da gudawa cuta ce dake yaduwa cikin yanayi mara tsafta kuma ayyuka ne ke haifar da su kamar ci ko shan gurbataccen abinci ko ruwa.Ya shawarci mazauna yankin dasu tabbatar dayin amfani da kayan tsafta ce bayan gida da kuma gudar gurɓataccen ruwa sha, babban taro na mutane ko tuntuɓar masu cutar amai da gudawa.
Sakataren ya kara da cewa sun sanya jami’an sa ido na cututtuka a kananan hukumomi 33 cikin shirin ko ta kwana don daukar matakan kariya a yankunansu.sannan Ya ce an sanya kwararrun masana kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu, don bada amsa ga barkewar cutar kwalara idan wani abu ya faru.
Adebisi ya ce, “Mutanen da ake zargi za a tura su asibitocin gwamnati mafi kusa don samun kulawa mai inganci.Hakanan kuna iya sanar da Ma’aikatar Lafiya ta kiran waɗannan lambobi: 09058704101, 08025245809. ”
Babban sakatare a ma’aikatar yada labarai, al’adu da yawon bude ido, Dakta Bunmi Babalola ya ce fadakarwar na da matukar muhimmanci duba da bukatar dakile yaduwar cutar.