An ayyana dan takarar jam’iyyar PDP a zaben kananan hukumomin Babbar birnin Tarayya Abuja da aka kammala jiya Asabar, Mista Christopher Zakka, a matsayin wanda ya lashe zaben karamar hukumar Abuja Municipal (AMAC).
Zakka ya samu kuri’u 19,302 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC Murtal Usman wanda ya samu kuri’u 13,240, a zaben, kamar yadda Jaridar Daily Post ta ruwaito.
A wani labarin Kuma Mai kama da wannan
Dan Takarar Jam’iyar PDP ya Lashe Karamar Hukumar Kuje
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shugaban karamar hukumar Kuje mai ci Abdullahi Suleman Sabo na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022.
Sabo ya doke sauran ‘yan takara biyar a dukkan shiyya 10 na yankin.
Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC mai kula da zaben kananan hukumomin Kuje, Sule Magaji ne ya sanar da sakamakon karshe a ofishin hukumar a safiyar yau Lahadi.
Ya bayyana cewa shugaban da ke kan karagar mulki ya samu jimillar kuri’u 13,301 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Sarki Hamidu Gaube na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 7,694.
Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a yankin, Loveday Ajo, ya samu kuri’u 79