Gwamnatin Amurka ta yi kira da a gudanar da sahihin zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa, inda ta ce za ta sanya idanu akan zaben domin ganin wadanda za su karya dokokin zabe.
Wannan kiran ya fito ne ta hannun jami’in hulda da jama’a na ofishin Amurka dake Nijeriya a Abuja. A cewar sanarwar, ya ce zaben da za a gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa yana da gayar muhimmanci ba kawai ga Nijeriya ba, hatta ga Afrika baki daya.
“Gwamnatin Amurka ba ta goyon bayan kowanne dan takara ko wata jam’iyya a zaben Nijeriya.” In ji Amurkar.
Amurkar ta ce; gwamnatin Amurka tana goyon dimokuradiyyar Nijeriyar. Inda ta kara da cewa sannan tana goyon bayan sahihin zabe, wanda za a gudanar da zaben cikin zaman lafiya.