Ramatu-Tijjani-Aliyu-2-594x400

Zaben Kogi: Ministar Abuja Ta Fitar Da APC A Kunya

Karamar ministar Abuja, Dr Ramatu Tijjani Aliyu ta kawo mazabarta ta Yagba dake gundumar Kakanda ga jam’iyyar APC a zaben gwamna da na Majalisar Dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma wanda aka fafata tsakanin Dino Melaye na PDP da Smart Adeyemi na APC wanda ya gudana a jiya Asabar a jihar Kogi.

Dr. Ramatu Aliyu, wanda kafin a zabe ta a matsayin karamar ministar Abuja, ita ce shugaban mata ta jam’iyyar APC.

Da yake ayyana sakamakon, jami’in INEC mai kawo sakamakon, Dr Okor Henry ya ce; dan takarar gwamna a APC ya samu kuri’a 350, a yayin da na PDP ya samu kuri’a 62 duk a mazabar Yagba din.

A bangaren masu takarar Sanata kuwa, dan takarar APC ya samu kuri’a 480, inda ya buge na PDP wanda ya samu kuri’a 53 kawai.

A gundumar Kakanda kuwa dake karamar hukumar Lokoja, dan takarar gwamna a APC ya samu kuri’a 5,631, yayin da na PDP ya samu kuri’a 1,109.

A bangaren Sanata kuwa, na APC ya samu kuri’a 4,907, yayin da na PDP ya samu kuri’a 2,013.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *