Sheikh AbdulHakeem Yayi-Akorede, Babban Limamin garin Akure dake jihar Ondo, ya shawarci ‘yan siyasa da su rungumi zaman lafiya kafin da bayan zaben fidda gwanin gwamna da za a yi a jihar.
Yayi-Akorede ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Akure a ranar Lahadi, a daidai lokacin da ‘yan siyasa ke shirye-shiryen zaben fidda gwanin gwamnan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC da PDP a jihar za su gudanar da zaben fidda gwanin gwamnan ne a ranar Litinin 20 ga watan Yuli da kuma 22 ga Yuli, a yayin da kuma za a gudanar da zaben gama gari na gwamnan jihar a ranar 10 ga watan Oktoba.
Babban Limamin ya nemi ‘yan siyasar da masu neman takara da su guji bangar siyasa da kuma aikata abin da zai dagula zaman lafiyar jihar.